Katsina Ta Tsakiya Ba Za Su Zaɓi Wanda Baya Zaune Cikin Su Ba. Hon. Sani Ɗanlami
Ɗan takarar kujerar majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya Hon Sani Aliyu Ɗanlami ya bayyana cewa babu yadda za a yi mutane su zaɓi wanda baya zaune cikin su.
Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya bayyana haka a wata hira da ya yi da kafar sadarwa ta yanar gizo DCL Hausa.
Ɗan takarar ya ƙara da cewa lokacin da yake ɗan majalisa wakilai na tarayya duk sati sai ya shigo Katsina domin ganawa da jama’arsa ta yadda zai ji irin matsalolin da suke fuskanta na yau da kullum.
“Shi abokin takara ta na jami’yyar PDP Hon. Aminu Chindo idan ya zo Katsina juma’a to Litinin yake komawa duk da cewar yanzu yaƙin neman zaɓe ake, ina ga ya ci zaɓe ai shikenan Abuja zai koma ” inji shi.
Haka kuma Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya bayyana cewa yana da abinda zai gayawa mutanen Katsina ta tsakiya domin su sake ba shi dama ya wakilcesu a majalisar tarayya a zaɓen 2023.
Ya ce mutanen Katsina su za su yi masa yakin neman zaɓe saboda irin abubuwan da ya yi masu a lokacin ya wakilci Katsina ta tsakiya.
“Ni ina da abin faɗa ga mutanen Katsina ta tsakiya a lokacin ina majalisa na samar da aikin yi ga matasa, inda na raba fiye da motoci 34 kuma waɗanda suka samu wannan kyauta suna nan da ran su.” Inji shi
Sannan ya ƙara da cewa ya damar da asibitoci guda uku domin sauƙakawa mata da gina gadoji har guda biyu da rijiyoyin burtsatse da tankuna masu ɗaukar lita 30,000 da tirelar siminti da kwanon rufi lokacin wani ambaliyar ruwa a Katsina.
Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya cigaba da cewa shi ya kawo hukumar kula da jarabawa ta NBAIS na ke nan Katsina inda har ya samu matsuguni na din din din, sannan ya samarwa matasa aiki duk a hukumar da sauran wurare.
Kazalika ya bayyana cewa ya samarwa matasa aiki a ma’aikatar shari’a da kuma kotuna, ya ce ya raba mashina 34 ga matasa kuma ya raba motoci ga Malaman Addini domin yaɗa da’awa.
Ya ce iya haka idan ya tsaya yana tabbacin mutanen ta tsakiya za su sake bashi dama, to balanta kuma al’umma na san jam’iyyar APC tun daga sama har ƙasa.
