September 18, 2026

Jadawalin Yadda Atiku Zai Ziyarci Jihar Katsina A Gobe Talata

0

Atiku Abubakar zai ziyarci jihar Katsina domin ƙaddamar da yakin neman zaɓen sa na shekarar 2023 sannan zai kai ziyara har wurare guda uku bayan inda zai ƙaddamar da takarar sa.

Babban daraktan yakin neman zaɓen jam’iyyar PDP na Katsina, Muhammed Mustapha Inuwa ya bayyana yadda wannan ziyara zata kasance a ya yin wannan taron manema labarai a Katsina

Dakta Mustapha Inuwa wanda yace “Dan takarar shugaban ƙasa zai zo Katsina domin gudanar da gangamin sa a ranar 20 ga Disamba, 2022.

Kafin gudanar da taron, zai ziyarci mahaifiyar marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua, da Sarkin Katsina, da ku a na Daura.

Taron zai gudana ne filin Wasa Na Muhammad Dikko da ke cikin garin Katsina inda bayan gama taron da kuma ziyara tawagar zata kama hanyar komawa Abuja kamar yadda aka tsara

Haka kuma DG din ya ƙara da cewa idan kuma aka samu wani canji bisa yadda aka tsara wannan taro za a bada sabuwar sanarwa.

Daga karshe Dakta Mustapha Inuwa ya ce ana sa ran fiye da motoci 4,000 ne za su yi wa Katsina tsinke domin yin lale marhabin ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *