Ambaliyar Ruwa: Gidauniyar “Matawalle Orphan'” Ta tallafawa Mutum 300 A Gasma
Daga Muhammad Maitela, Damaturu
Gidauniyar ‘Matawalle Orphan’ a ƙarƙashin ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Karasuwa a jihar Yobe, Hon. Adamu Dala Dogo (Matawallen Nguru), ta tallafawa magidanta 300 waɗanda ibtila’in ambaliyar ruwa ya shafa a garin Gasma da ke ƙaramar hukumar.
Sa’ilin da yake ƙaddamar da bayar da tallafin ga al’ummar garin, Manajan Daraktan Gidauniyar Matawalle Orphan, Mohammed Musa Gasma ya ce kimanin mutum 300 ne suka ci gajiyar tallafin kuɗin.
Inda ya kara da cewa, “Waɗanda gidajen su ya rushe baki ɗaya mun tallafa musu da 10,000, yayin da waɗanda gidajensu rabi ko kuma ambaliyar ta shafi wani ɓangare na gidajensu mun taimaka musu da gudummar 5000.”
“Sannan kamar yadda muka saba, ayyukan wannan gidauniyar ya shafi taimaka wa marayu ne da maras galihu a cikin al’umma.
Wanda idan mun lura jama’ar wannan yanki sun fuskanci ƙalubale n ambaliyar ruwan da ya jefa daruruwan mutane cikin tsananin rayuwa, kuma bisa hakan muka ga ya dace mu tallafa musu da dan abin da ba a rasa ba.”
Mohammed Musa ya ƙara da cewa, ta la’akari da gidauniyar su ta yi, wanda ko shakka babu jama’a suna buƙatar kowane irin tallafi ne, saboda yadda ambaliyar ruwan ta lalata gidaje da amfanin gonakin jama’a.
Ya ƙara da cewa, “Saboda haka a matsayin mu na gidauniyar da ba ta gwamnati ba, kuma muna da ayyukan jinƙai da dama da muke a fannin tallafa wa marayu da masu ƙaramin karfi, shi ne muka ga ya dace mu taimaka wa waɗanda suka fuskanci ibtila’in ambaliyar ruwan.”
“Abu na biyu- kuma, waɗannan ayyukan jinkan suna gudana ne daga aljihun Hon. Adamu Dala Dogo (Matawallen Nguru), kana ɗan majalisar dokokin jihar Yobe, mai wakiltar ƙaramar hukumar Karasuwa. Ya kafa wannan gidauniyar ne domin taimaka wa marayu da masu ƙaramin karfi a cikin al’umma.” In ji shi.
Har wala yau, S’shugaban gidauniyar, ya buƙaci waɗanda suka ci gajiyar tallafin kuɗin da cewa su ci gaba da addu’o’in Allah ya kawowa jihar Yobe da Najeriya baki ɗaya dawamamen zaman lafiya.
Haka kuma ya yi wa al’ummar fatan alheri da samun cikakken zarafin sake gina gidajensu tare da mayar da gurbin abubuwan da suka yi asara ta dalilin ambaliyar ruwan.
A hannu guda kuma, waɗanda suka samu tallafin; maza da mata sun bayyana matuƙar godiya tare da yaba wa gidauniyar bisa duba da yanayin da suke ciki da basu tallafin inda suka roki Allah ya sakawa wanda ya assasa gidauniyar da masu gudanar da ita da mafificin alheri.
