Kungiyar Arewa Youths Forum Ta Karrama Shugaban Gidauniyar SDA A Katsina
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Kungiyar Matasan Arewa (Arewa Youth Forum) ta zabi shugaban gidauniyar SDA Alhaji Shamsu Dahiru Ahmad (SDA) tare da karrama shi da kambun jarumta na (SARDAUNA GOLDEN MEDAL) a turance.
Wannan karrama na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban gidauniyar ya dukufa wajan ganin ya tallafawa marasa karfi akan abinda ya shafi kowa masu sana’o’I tare da ba su jari domin dogaro da kai.
Idan za a iya tunawa Alhaji Shamsu Dahiru Ahma (SDA) ya sha bayyana cewa wannan gidauniya tasa ba ta siyasa ba ce, an kafa ta ne domin taimakawa marasa karfi kuma kofa a bude take ga duk wanda ya ke da niyyar tallafawa masu karamin karfi.
Da yake Jawabi wakilin Shugaban kwamitin Amintattu na Kungiyar Amb. Umar Lawal ya bayyana cewa Jarumta da sadaukar da Kai ga al’umma shine dalilin da yasa suka zabi Alh. ShamsuDahiru Ahmad (SDA) da wannan karrama wa.
Ya bayyana shugaban gidaunaiyar a matsayin jagora, shugaba Mai tausayin al’umma da kowace irin al’ummake fatan samu domin bada gudunmawa wajan cigaba ta fannoni daban-daban da suka hada ilimi da tarbiya da sana’o’I da sauransu.
Tun farko da yake jawabin maraba Mal. Abdulaziz Idris Gangara Wanda shine shugaban kungiyar ta AYF a matakin jihar Katsina, ya bayyana dalilan zabar Alh Shamsu Dahiru Ahmad (SDA) da wannan girmamawa, ya yi godiya ga Allah da ya nuna masa wannan rana
“Wannan kungiya ta zabi Alh Shamsu Dahiru Ahmad (SDA) bisa ga irin gudunmwar da yake badawa wajen cigaba da taimakon al’umma, kama daga koya sana’o’i ga Mata da Matasa, tallafin karatu, tallafi ga Dattawa da masu matsakaitan karfi.” Inji shi
Haka kuma ya kara da cewa kowace al’umma tana bukatar hazikan mutane masu son cigaba da kishi irin Alh Shamsu Dahiru Ahmad (SDA) wanda zai tsamowa jama’arsa kitse daga wuta”
Shima da yake nasa jawabin Sakataren kungiyar ta Arewa Youths Forum ” ya yi ya bo da godiya ganin yadda Alh Shamsu Dahiru Ahmad (SDA) yake tsaye wajen taimakon al’umma babu dare ba rana.
Wannan taro dai wanda ya zama wani baban tarihi ya samu halartar manyan baki da ‘yan uwa da baokan arzik da kuma wakilan kungiyar Arewa Youth Forum na jihar Katsina
