Wasu Fusatattun Matasa Sun Bankawa Fadar Iree Oba Wuta A Jihar Osun.
Da yammacin jiya Alhamis ne wasu fusatattun matasa suka yi ɓarna a fadar Aree na Iree da ke karamar hukumar Borripe ta Arewa a jihar Osun.
An bayyana cewa, wasu matasa ne suka kona fadar da ba su ji dadin kamen da jami’an tsaro suka yi ma Aogun na Iree, Cif Soliu Atoyebi a ranar Alhamis ba.
Matasan sun dira wurin, tare da ƙona fadarshi da misalin karfe 7:00 na dare, lokacin da aka ce basaraken gargajiyar, Oba Ponle Ademola, ba ya cikin fadar.
Lamarin dai ya janyo toshewar manyan hanyoyin shiga garin, yayin da matasan da suka fusata suka yi ta kone-kone a kan hanyoyin.
An bayyana cewa masu harkokin kasuwanci a garin sun kulle shagunansu, yayin da mazauna garin su ma suka koma gidajensu don dalilan tsaro.
Ba’a samu kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun SP Yemisi Opalola ba domin cewa wani abu, saboda wayarshi kashe take.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa, Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun bayan kwana ɗaya da rantsar da shi, ya bayar da umarnin bangaren zartarwa na jingine nadin wasu sarakunan gargajiya uku da suka haɗa da: Aare na Iree; Akirun na Ikirun da Owa na Igbajo.
Adeleke ya kuma bada umarnin a kulle fadar sarakunan gargajiyan uku, inda jami’an tsaro su riƙa kula da fadojin domin hana karya doka da oda.
An ta samun fargaba a cikin garin Iree biyo bayan nada Prince Ponle Ademola a matsayin Aree of Iree da tsohuwar gwamnatin Gboyega Oyetola ta yi, inji majiyar Popular News Hausa ta Vanguard.
Wasu gidajen sarauta da kungiyoyi a garin sun ƙi amincewa da zabo Ademola da aka yi, inda suka yi zargin cewa jami’an gwamnatin Oyetola ne suka dora ma mutanen jihar shi.
