Gwamnatin Zamfara Ta Koka Da Gangamin Ɗan Takarar Gwamna Na Jam’iyyar PDP
Daga Hussaini Ibrahim, Gusau
Gwamnatin Jihar Zamfara ta koka da Zargin ɗan takarar gwamna jami’yyar adawa ta PDP, da Cutar da al’ummar da lalata kayan gwamnati da na jam’iyyar APC a lokacin da su ke gudanar da gangamin sa a ranar lahadi da ta gabata.
Mataimakin gwamna, Sanata Hassan Nasiha ne ya bayyana haka ga manema labarai a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Sanata Nasiha ya bayyana cewa, a kwanakin baya masu neman kujerar Sanata a Zamfara ta yamma , tsohon gwamna Abdulaziz Yari da Satana Kabiru Marafa, mai neman takarar Sanata a Zamfara ta tsakiya, sun gudanar da gangamin su lafiya batare da an lalata kayan gwamnati ba ko na wata Jamiyya ba.
Amma sai gashi ɗan takarar gwamna na PDP da Kotu ta haramtamasa takara ya gabatar da gangamin wanda yayi sanadiyar asarar dukiyoyin da kayan al’umma. Inji Nasiha.
” Dan haka Gwamnati bazata zura idanu ba akan haka ba kuma zata ɗauki mataki akan duk Wanda ke neman hana zaman lafiya da bata dukiyoyin al’umma.inji Muƙaddashin gwamna Matawale, Sanata Hassan Nasiha.
