November 19, 2026

Babu Inda Zuri’ar Malam Ummarun Dallaje Bata Kai Ba Cikin Duniya.

0

An Ƙaddamar da littafin mai suna Katsina Gidan Dallaje

Shi ne Sarkin Fulani Na farko A Masarautar Katsina

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Zuri’ar Malam Ummarun Dallaje na cigaba da bunƙasa a fadin duniya musamman idan aka yi la’akari da yadda zuri’ar ke ƙoƙarin haɗa kan iyalan na su wuri guda.

Bikin ƙaddamar da littafi Mai suna Katsina Gidan Dallaje wanda ya gudana ya ƙara fitowa da ƙima da kuma martabar wannan gida mai dogon tarihi a masarautar Katsina.

Da yake jawabi ɗaya daga cikin waɗanda suka rubuta littafin tarihin Katsina Gidan Dallaje Malam Suleiman Saulawa ya ce “Babu inda zuri’ar Malam Ummarun Dallaje ba su kai ba a wannan duniya, saboda haka ya ce ƙaddamar da wannan littafi yana matsayin wani abu mai matuƙar mahimmanci ga Dallazawa.

Sannan ya bayyana Mallam Ummarun Dallaje a matsayin wani mutum wanda ya kasance ginshiki da ya bada gudunmawa wajan cigaban masarautar Katsina a lokacin da yake raye.

Suleiman Saulawa ya cigaba da cewa Malam Ummarun Dallaje shi ne Malami na 39 a lokacin rayuwar sa, sannan ya kasance mutum guda ɗaya tilo da ya hidimtawa addinin Musulunci.

Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da suka sanya zuri’ar Malam Ummarun Dallaje ke so a musanya sunan filin Kangiwa da ke Kofar Soro (Fadar Sarkin Katsina) da sunan Malam Umaru Dallaje

Dallazawa dai suna kira ga gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari da ya nunawa zuri’ar Malam Ummarun Dallaje ƙaranci ta hanyar sauya sunan filin Kangiwa zuwa Malam Ummarun Dallaje.

” Kimanin shekaru 30 ke nan muna ƙoƙarin samar da wannan littafi na Katsina Gidan Dallaje da zummar ya zama wani tsani na haɗa kan zuri’ar Malam Ummarun Dallaje tare da taimakawa masu ƙaramin karfi” inji Saulawa

Haka kuma ya ƙara da cewa baban dalilin da yasa aka wallafa wannan littafi da Hausa shi ne domin a sanar da matasa masu tasowa tarihin Dallazawa saboda wannan shi ne karo na farko da aka yi da Hausa.

Sannan sai ya bada tabbacin cewa duk abinda aka samu wajan ƙaddamarwar za a yi amfani da shi ne wajen bunƙasa cibiyar gidan Yarima da ke Sararin Kuka cikin birnin Katsina domin amfanin zuri’ar Malam Ummarun Dallaje.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *