Iftila’in Gobara: Hon. Sani Aliyu Ɗanlami Ya Kai Ɗauki Ga Waɗanda Bala’in Ya shafa
Ɗan takarar kujerar majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya Hon Sani Aliyu Ɗanlami ya kai ziyara jaje tare da bada tallafi ga al’ummar da iftila’in gobara ya shafa a cikin birnin Katsina.
A jiya talata ne, aka wayi gari da iftila’in gobara a wani ɓangare na Babar kasuwar Katsina inda aka tabka asara ta miliyoyin nairori
Sannan a kwanakin baya tashar motar NARTO ita sun fuskanci irin wannan gobara inda wasu shaguna da kayayyakin da ke cikin suka kone kurmus.
Ɗan takarar dai ya jajanwa shuwagabannin kasuwa da kuma tashar motar NARTO tare da ba su tallafi kuɗi Naira dubu dari takwas (N800,000) a matsayin tasa gudummawar.
Kazalika an raba kuɗin kamar haka, a ya yin da ‘yan kasuwa suka samu dubu dari biyar su kuma na NARTO suka samu dubu dari uku.
Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya bayyana wannan iftila’in gobara a matsayin ƙaddara daga Allah ta’ala wanda ya ce Allah zai mayar masu da mafiyin abinda suka rasa
Da suke maida jawabi dukkansu shuwagabannin kasuwa da kuma tashar NARTO sun yi godiya da wannan ziyara ta jaje da Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya kai kuma shi ne ɗan siyasa na farko da kai irin wannan ziyara
