Ɗan takarar gwamna ya ci akwashin ceto Katsina da ga matsalar rashin tsaro
Dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP a jihar Katsina, Ibrahim Zakari, ya yi ci alwashin ceto jama’a daga matsalolin tsaro da zamantakewa, idan aka zabe shi gwamna a 2023.
Zakari ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke kaddamar da yakin neman zaben sa na gwamna a ofishin jam’iyyar SDP na Katsina a yau Asabar.
“Buri na na zama gwamnan jihar Katsina ba don mulki ba ne, sai dan in yi wa al’umma hidima.
“Manufofin jam’iyyarmu sun dogara ne kan bukatar karfafa mutane ta hanyar bunƙasa ilimi, kiwon lafiya, noma, kayayyakin more rayuwa da sauran bangarorin tattalin arziki.”
“Ina da kwarewar da ake bukata don samar da ingantaccen shugabanci a wannan lokacin da jihar ke fuskantar kalubalen zamantakewa, tattalin arziki da matsalar tsaro da yawa,” in ji shi.
Dan takarar gwamnan ya bayyana wasu daga cikin manufofinsa guda bakwai da suka hada da ilimi, raya karkara, karfafa matasa da mata, da noma da sauran muhimman batutuwa.
“Na zo nan ne domin in ba da gudummawa ta, a matsayina na ɗan asalin Jihar Katsina. Ba wai ina takara ne kawai don in karbe mulki daga hannun jam’iyya mai mulki ba, sai dai don ceto al’ummar jihar.
“Kowa ya san halin da kasar nan ta samu kanta. Ba za mu iya yaudarar kanmu cewa komai na tafiya daidai ba. Shi ya sa na ke cikin takara, dole ne mu hada karfi da karfe don ceto mutanenmu,” ya kara da cewa.
