Kwamishinan Wasannin Jihar Katsina Ya Bukaci Kwamitin Da Zai Tantance Yan Wasan Da Aka Gayyato Ya Yi Gaskiya.
Kwamishinan kula da harkokin wasannin jihar Katsina ya hori kwamiti mai zaman kanshi da tawagar kwararru da za su tantance yan wasan ƙwallon kafar da aka gayyato su saka gaskiya wajen zaƙulo masu hazaka.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in watsa labaran hukumar gudanarwar kungiyar Kwallon kafar Nasir Gide ya fitar.
Dr. Bishir Gambo ya fadi hakan ne a lokacin da yake duba yadda ake tattara takardun yan wasan da aka gayyato domin tantancewa.
Ya bukaci yan wasan da aka gayyato su yi amfani da damar da aka basu su nuna da’a a lokacin aikin tantancewar da kuma zaƙulo masu hazaka daga cikinsu.
Kwamishinan dai ya samu rakiyar daraktan wasanni, jami’in Katsina United da sauran masu ruwa da tsaki a lokacin duba shirin.
Sanarwar ta ce, yan wasan 120 da aka gayyato za a rabu gida 8, kuma kowane gida ɗaya nada mutane 15 domin samun damar zabo wanda ake so ta hanyar bada horo da wasan sada zumunta.
