Yadda Taron Taya Murnar S.A Babangida Kayawa Ya Gudana
Da yammacin jiya laraba ne matashin dan siyasar nan Hon Babangida Kayawa kuma na hannun damar Sen. Yakubu Lado Danmarke, dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar PDP ya shirya tare da hada gagarumar walima ta cin abinci domin taya shi murna akan matsayin da Allah Ya bashi.
Hon. Babangida dai ya samu mataimaki na musamman a harkar kafofin sadarwa na zamani (S.A Social Media), na tafiyar gidan Sen. Yakubu Lado Danmarke.
Kayawa ya hada wannan walima ne domin nuna jin dadin sa da godiya akan irin wannan karramawa da mai gidan shi ya yi mashi domin taimaka mashi ta hanyoyi da dama na kafar sadarwa ta social media da sauran hidimomin da suka shafi siyasar shi.
Haka ya tara jajirtattun matasa aka ci aka sha, kuma aka gudanar da addu’o’i na musamman domin Allah ya shiga lamarin, da tunarar da shi muhimmancin shugabanci da irin nauyin da ya rataya a wuyan sa.
Da yake tofa albarkacin bakinsa daya daga cikin fitatu kuma jajirtatun Matasa jam’iyyar PDP masu amfani da kafar sadarwa ta zamani wato Nuraddeen Adam Kankara Tina ya yi fatan samun nasara a wannan tafiya.
Popular News Hausa suna yi maka Fatan Allah ya yi mana jagora. AMIN
