Gwamna Bagudu Ya kori Duk Kwamishininsa Baki Ɗaya
Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya kori gaba daya kwamishinoni da sauran jami’an da ke majalisar zartaswar jihar.
A cikin sanarwar da sakataren gwamnatin jihar ya fitar, Bagudu, ya gode musu, sannan ya ce zai mayar da wasu daga cikinsu a sabuwar majalisar jihar ta Kebbi da za a sanar nan ba da jimawa ba.
