An Tsinci Gawarwakin Daliban Jami’ar KWASU a Dakin Kwanan Dalibai.
An tsinci gawarwasu dalibai biyu na Jami’ar Jihar Kwara wato KWASU, Malete, Tobiloba Daniel tare da wadda ake zargin masoyarsa ce mai suna Arewa Abayomi a dakin Daniel, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa wadanda suka mutun dukkansu dalibai ne yan aji 2, kuma suna rubuta jarabawa ne a lokacin da lamarin ya faru.
A cewar wani ganau dalibin KWASU da ya nemi a sakaya sunansa ya ce: “Muna zargin masoya ne kuma mun damu da ba mu gansu a lokacin jarrabawa ba har tsawon kwana 3.
“A lokacin da wasu abokansu suka je dakin kwanansu da ke wajen makarantar suka same su a mace kuma tsirara.”
Da take mayar da martani kan lamarin, Daraktar hulda da jami’ar jami’ar KWASU Dr. Saeedat Aliyu, ta ce babu wata sanarwa a hukumance kan lamarin.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ajayi Okasanmi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce: “Bayanan an ga gawarsu a cikin dakinsu, kuma an sanar da ‘yan sanda.
“Jami’an mu ne suka balle kofar sannan aka kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin domin yin abinda ya kamata.
“Ana ci gaba da bincike kan lamarin,” in ji Okasanmi.
