Wani Ya Kashe Abokinsa Saboda Ya Sawo Mota A Jihar Kogi.
Jami’an ‘yan sandan jihar Kogi sun kama wani matashi mai matsakaicin shekaru da ya kashe abokinsa Kehinde Ajayi, tare da binne gawarsa a gidansa da ke unguwar Felele a Lokoja, babban birnin jihar, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta Vanguard.
Wanda ake zargin an ce ya kashe Ajayi ne a ranar 24 ga watan Yuli na 2022, bayan da ya siyo mota kirar Toyota Sienna mai lamba LSD 228 HJ.
‘Yan sanda sun ce mutumin da aka kama mai gyaran AC, ya yaudari marigayi Kehinde ne da misalin karfe 10 na safiyar ranar da lamarin ya faru don ya tafi da shi domin yin murnar zuwan sabuwar motar da Kehinde ya saya.
An bada rohoton cewa, marigayi Kehinde, wanda ake zargin da kuma wasu mutane sun je wani wuri ne domin yin murnar zuwan sabuwar motar, amma daga nan ba a sake ganin su ba.
‘Yan sanda sun ce: “Lokacin da iyalan marigayi Kehinde suka kai karar dan uwansu da ya bace ga ‘yan sanda, an kama daya daga cikin abokansa (mai laifin) a makon da ya gabata kuma ya yi bayanai masu amfani game da abin da ya faru da marigayi Kehinde. Bayan kashe shi, wanda shi ne ake zargin ya tafi da motarsa.”
Sai dai a ranar Litinin, wanda ake zargin ya kai ‘yan sanda gidansa don gwada masu inda ya binne gawar Kehinde.
Bayan haka ne dai, matasan da suka fusata suka kai farmaki gidan wanda ake zargin bayan da ‘yan sanda suka fito da gawar daga gidan.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, SP William Ayah, ya ce an gano gawar marigayi Kehinde, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo sauran da suka taimaka wurin aikata laifin.
