Kungiyar Tsoffin Daliban Makarantar Firamaren Usman Liman Musawa Ta Kafa Kwamitin Kiwon lafiya.
Kungiyar tsoffin ɗaliban makarantar Firamaren Usman Liman Primary School Musawa ta kafa kwamitin kiwon lafiya, kula da marayu da kuma taimaka ma makarantar don amfanin tsoffin ɗalibai.
Shugaban kungiyar Babangida Usman ne ya bayyana hakan a lokacin taron tsoffin daliban makarantar na shekarar 1992.
Ya ce makarantar ta yaye manyan mutane da dana a cikin kasar nan.
Saboda shugaban kungiyar ya yi kira ga tsoffin daliban makarantar da su taimaka ma kokarin gwamnati wurin bunkasa Ilimi tun daga tushe.
Shima da yake magana sarkin Musawan Katsina hakimin Musawa Sagir Abdullahi Inde ta bakin wanda suka wakilce shi, ya yaba ma hangen nesan tsoffin daliban na kafa ƙungiyar.
Inda ya yi kira a kafa kungiyar iyaye mata domin ci gaban makarantar baki daya.
Daga nan dai, shugaban kwamitin kula da marayu Shehu Bawa Musawa ya bada gudunmawar naira ₦100,000 ga kwamitin.
