September 18, 2026

Gwamnonin PDP Sun Yi Magana Kan Taron Tuntuba Da Aka Yi A Paris Da Landan.

0

Gwamnan jihar River Nyesom Wike da takwarorinsa na Benue da Abia, Samuel Ortom da Okezie Ikpeazu sun ce ganawar da suka yi a London da Paris tare da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party Peter Obi da kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP duk wani bangare ne na tuntubar juna fiye da muradun jam’iyyar da aka tsara don ceto Najeriya daga kalubalen da ke mata barazana, inji majiyar Popular News Hausa ta AIT.

Da yake magana bayan sun isa filin jirgin sama na Fatakwal a ranar Juma’a, Gwamna Wike ya ce ba a cimma wata kwakkwarar yarjejeniya ba a tattaunawar da ya yi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, amma ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa.

Bayan gudanar da tattaunawar a London da Paris, gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu, Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom da kuma gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike sun dawo Najeriya.

Jirgin su daga Landan ya sauka ne a filin jirgin sama na Fatakwal da misalin karfe biyu na rana.

Gwamna Wike da mambobinsa sun yi ganawar daban da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party Peter Obi.

Sun ce Najeriya na cikin kunci kuma tana matukar bukatar taimako daga kowane bangare.

Gwamnonin sun ce za su fadada tuntubarsu a gida da waje.

A tsokacin zoyarar dai an gwamna Wikke da tawagarsa a karo na farko suna gunawa da dan takarar shugaban kasa a inwar jam’iyar PDP.

Sai dai Gwamna Wike ya bayyana cewa babu wata tabbatacciyar yarjejeniya a lokacin zaman tattaunawar.

Ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da wasu ‘yan siyasa masu son zuciya da basu son hadin kan kasa ba.

Nyesom Wike ya ce, ba zai ji tsoron dukkan wata barazana ba.

Kuma yayin da suke komawa gida domin yin shawarwari masu zurfi kan yadda za a ceto Najeriya, Gwamna Nyesom Wike, Gwamna Samuel Ortom da kuma Gwamna Okezie Ikpeazu, sun ce akwai sa-ran abubuwa za su gyaru a Najeriya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *