Zaben 2023: Sama da Mambobin APC Da PDP 7,000 Suka Sauya Sheka Zuwa NNPP.
Sama da mambobin jam’iyyar PDP dana APC dubu bakwai ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP a wannan Juma’ar a jihar Oyo gabanin babban zaben 2023.
Majiyar jaridar Popular News Hausa ta AIT ta bayyana cews, Dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP Engr Popoola Joshua wanda ya karbi sabbin mambobin a fadin kananan hukumomin jihar 33 tare da shugaban jam’iyyar Adebisi Olopoenyan ya ce hakan ya kara tabbatar wa ‘yan Najeriya takaicin dake cikin manyan jam’iyyun biyu.
