September 17, 2026

Hon Salisu Yusuf Majigiri: Agogo Sarkin Aikin…

0

Daga Shafin BAKORI

Mai girma Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar katsina H.E Salisu Yusuf Majigiri Garkuwan Gabas din Katsina Wazirin Iyan Katsina Hakimin Mashi kuma jagoran tarwatsa kungiyar APCsic ta jahar katsina.

Ya samu zama da wasu kungiyoyi da suka kawo mashi ziyarar ban girma da nuna goyon baya ga jam’iyyar PDP tun daga matakin mazabu har zuwa matakin tarayya.

Kungiyoyin sun hada da.

1-PDP youth Mobilization and awareness forum.

2- Katsina youth ideology for PDP collaborate.

3 – PDP Modern singer.

Kungiyoyin sun jaddada ma jam’iyyar PDP goyon baya tare da yimata aiki tukuru domin ganin sun kauda jam’iyyar APC daga karagar mulki tare da ceto kasa daga hannun mulkin zalunci.

A jawabin kungiyoyi sun tabbatar ma Shugaban jam’iyyar PDP na jihar katsina cewa a shirye suke da suba jam’iyyar PDP dukkan gudummuwa domin ganin tayi nasara a zabe mai zuwa.

Mai girma Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar katsina H.E Salisu Yusuf Majigiri Garkuwan Gabas yayi godiya ga yayan kungiyoyin da suka kawo mashi ziyarar ban girma tare jaddada masu cewa yana tare dasu kuma jam’iyyar PDP zatayi aiki dasu ka fada da ka fada, Kuma sannan Shugaban jam’iyyar PDP na jihar katsina yaja hankalin matasa da su shigo harkar siyasa da gaske domin a dama dasu suma su taka rawar gani, har ila yau ya Kara jaddada ma matasa kwarin gwiwa akan mahimmanci shiga harkar siyasa da kuma tsayawa takarar a kujerun siyasa ba tare da jin tsoro bah ko cewar sai ka samu kudi zakayi takara.

Shugaban yayi Kira da mu tashi tsaye musamman mu matasa wajen ganin cewa mun shigo harkar siyasa domin zaba ma mutane nagartaccen Shugaba da zai jagoranci talakawa a kowane mataki domin fiddo kasar mu daga kangin da jam’iyyar APC ta jefa talakan kasar nan.

Daga karshe yayi godiya ga dukkan kungiyoyin.

A tare da Shugaban jam’iyyar PDP na jihar akwai Mataimakin shi Hon Salisu Lawal Uli, akwai Legal Adviser Hon  Brr Mustapha Mahuta, akwai Noth west Youth Leader Hon Hamza Jibia, Kuma Hon Hamisu Gambo Danlawan Katsina.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *