Ba Mu Goyi Bayan Ayyukan ‘Yan Sakai Ba a Harkar Tsaron Jihar Katsina. – Masari
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari Ya bayyana cewa ba su goyi bayan ayyukan ‘yan sakai ba a cikin harkar tsaro ba saboda su ‘yan sakai tashi suke daga wani gari zuwa wani gari suna farautar ‘yan ta’ada.
Aminu Bello Masari yana wannan magana ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Katsina dangane da batun da ya shafi harkar tsaro da kuma zaban kananan hukumomi da gwamnan ya ce nan ba dadewa ba za a gudanar da shi a jihar Katsina
A cewar gwamnan ‘yan banga kuwa su daman ‘yan gari ne kuma garin suke tsarewa, amma bai yuwa mutun ya tashi daga Katsina ya tafi Mai’adua farautar dan bindiga shi mutumin Mai’adua me yake yi?
“Kowa zai yi farautar tsaro ya yi a garinsu, inda ya sani aka san shi wannan shi ne abinda shari’a ta yarda da shi har ta Allah. kowa ya tashi ya tsare kanshi, kuma wanda duk suka zo da hanyar taimako, zamu taimaka masu, hukumomin ‘yan sanda a shirye suke su taimaka duk wani makami a yi masa rijista” inji shi
Kazalika gwamna Masari ya yi bayanin cewa ba fa za a zura ido a tafi a haka ba, ya ce rokon da suke yi wa Allah yadda suka samu kasar nan cikin tashin hankali, to in Allah ya yarda ba za su baiwa masu zuwa ba cikin wannan tashin hankalin ba, sai dai cikin kwanciyar hankali.
Haka kuma ya yi tambihin halin tsaro da ake cikin a jihar Katsina inda ya bayyana cewa idan za a yi wa abin adalci an samu cigaba a jihar Katsina da wasu jihohi duk da cewa abin ya tsananta a jihar Sakwato a wasu kananan hukumomi guda biyu.
Ya ce hatta ita kanta kasar an dan samu sauki, abinda ke nan, shi ne ya ya za a gina hanyar da za a dawo da al’amura yadda suke ada ko kuma kusan yadda suke.?
