‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Wani Tashin Hankali Tsakanin Jami’anTa Da Yan Achaba A Abuja.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da wani tashin hankali tsakanin jami’anta da masu sana’ar achaba a gundumar Durumi dake Abuja.
Majiyar Popular News Hausa ta jaridar Sunnews ta ce, Rikicin dai ya biyo bayan aiwatar da dokar hana babura ne a birnin tarayya, wanda aka yi bayan gudanar da zama daban daban da shuwagabannin masu sana’ar achabar.
A jiyaTalata ne rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta fara dabbaka dokar domin tabbatar da bin umarnin doka.
A lokacin dabbaka dokar, ‘yan sanda sun kama yan achaba 20 da suka karya dokar.
Rikicin dai ya faro ne lokacin da aka kai baburan ofishin ‘yan sanda daga bisani kuma za a mika su ga hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa, wadda aka fi sani da VIO domin tantance su.
Da suka ga jami’an VIO sun iso ofishin ‘yan sandan, sai masu baburan suka yanke shawarar hana su fita daga ofishin yan sandan, tare da fatattakar su.
Rundunar ‘yan sandan dai ta dauki matakin tarwatsa masu achabar da suka fito kan tituna domin nuna rashin jin dadinsu.
Ko da yake ba a yi asarar rayuka ko dukiyoyi ba, saidai wadanda suka jikkata a lokacin dauki-ba-dadin.
