September 18, 2026

An Bada Kwangilar Hanyar A Batagarawa — Bala Garba Tsanni.

0

Shugaban karamar hukumar Batagarawa ya ce an bada kwangilar shinfida hanyar da ta haɗa cikin garin Bakiyawa da gadar dake garin.

Bala Garba Tsanni wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake yin jawabi a wurin da za a yi aikin, ya ce bada jimawa za a shinfida hanyar ta yadda masu motoci za su riƙa bin ta lafiya lau.

Ya ce hanyar nada mahimmanci ga mutanen yankin.

Ya yi kira ga yan kwangilar da za su yi aikin da cewa su yi shi cikin lokacin da aka ba su.

Haka kuma, shugaban karamar hukumar ya kai ziyarar duba aikin ginin wani sansanin soji da ake ginawa a Barawa.

Da suke maida jawabi a madadin al’ummar wurin, Malam Abbas da malam Mustapha Bakiya sun yaba ma shugaban karamar hukumar bisa kawo ziyarar.

Shima shugaban jam’iyyar APC na yankin Shamsu Bambani ya bayyana jin dadi bisa ayyukan, tare da yin kira ga mutane su mallaki katin zabe.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *