Sakataren Ilimin Karamar Hukumar Mashi Ya Ce Shirin Ba Yan Makaranta Abinci Na Sanya Su Zuwa Makaranta.
An bayyana shirin ciyar da yara yan makarantar primary a matsayin abinda dake sa su zuwa makaranta, da kuma ƙara kwazonsu a karamar hukumar Mashi.
Sakataren ilimin karamar hukumar Mansir Ali Mashi ya bayyana hakan ga manema labarai a Mashi.
Mansir Mashi ya ce sama da yara 21,000 ne ke amfana da shirin ciyar da yan makarantar a yankin.
Haka kuma, ya yaba ma kokarin gwamnatin tarayya, da gwamnatin jihar Katsina, hadi da hukumar bada ilimin bai daya bisa ba masu aikin dafa abinci kudin aikinsu don ganin shirin ya ci gaba da tafiya ba tare da wata matsala ba.
Ya ce, a kokarin ganin an inganta ilmin makarantun primary a yankin, wata tawagar bincike daga Abuja ta kai ziyara yankin don duba makarantun yankin, da kuma samun bayanan malamai da dalibai.
Sakataren ilimin ya kara da cewa, tawagar za ta kuma kewaya zuwa makarantun primaryn 87, hadi dana Islamiyyu dake yankin.
A wani labarin kuma, an bukaci wadanda suka isa kada kuri’a a karamar hukumar Mashi da su je su mallaki katin zabe a cikin sauran kwanakan da suka rage na kammala aikin rijistar katin zaben.
Shugaban hukumar hukumar Salisu Kallah ya yi wannan kiran a lokacin kaddamar da shirin wayar da kan mutane kan su mallaki katin zabe a matakin mazabu da karamar hukumar.
Shugaban karamar hukumar ya bada tabbacin bada goyan bayan shi ga masu aikin rijistar a yankin don ganin an samu nasara.
A jawabin shi babban jami’in hukumar zaben a yankin Mr. Godwin ya yi kira ga mutane da cewa su yi amfani da karin lokacin da aka yi su yi rijistar katin zaben ga wanda basu da shi.
Ya kuma yi kira ga wanda basu amshi nasu ba, da cewa, su je su amsa.
A nashi bangaren iyan Katsina hakimin Mashi Alhaji Kabir Aminu ya bayyana cewa katin zabe ne ke bada damar a zaɓi shugabanni na gari.
