September 18, 2026

Sanatan Arewacin Yobe: Al’ummar Bade Da Jakusko Sun Goyi Bayan Bashir Machina

0

Daga Muhammad Shamsudeen, Yobe

A lokacin da taƙadama ke ci gaba da zafafa tsakanin shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan, da ɗan takarar Sanatan Arewacin Yobe, Hon. Bashir Sharif Machina; biyo bayan kayen da Sanata Lawan ya sha a zaɓen fidda-gwani shugaban ƙasa da jam’iyyar APC ta gudanar a makon da ya gabata da kuma nasarar zaɓen fidda-gwani da Machina ya samu a ɗaya ɓaren.

Wasu majiyoyi sun nuna cewa har yanzu Hon. Lawan ya na hararar kujerar tare da bayyana buƙatar Hon. Bashir Sharif Machina ya janye masa, bayan lashe zaɓen fidda-gwani takarar Sanatan Arewacin Yobe, al’amarin da ke ci gaba da ɗaukar hankulan ‘yan Nijeriya.

A daidai wannan gabar, al’ummar ƙananan hukumomin Bade da Jakusko a yankin da ke jihar Yobe sun fito kan tituna domin bayyana goyon bayan su ga takarar Hon. Machina, a tsakiyar wannan mako (ranar Asabar) a garin Gashuwa, shalkwatar karamar hukumar Bade.

Dubban jama’ar sun ziyarci fadar Sarkin Bade; Mai martaba mai Abubakar Umar Suleiman domin miƙa gaisuwar girma tare da bayyana maƙasudin taron, wanda ya kunshi mata, matasa da masu ruwa da tsaki a siyasar yankin.

Da yake bayani ga manema labaru jim kaɗan da kammala taron, Barista Hamza Hashimu Karage, ya bayyana cewa, a matsayinsu na al’ummar masarautar Bade, sun yaba da hidimar da Sanata Ahmed Lawan ya yi wa ƙasa na kimanin shekaru 16 a zauren majalisar dattawan Nijeriya, inda har Allah ya kai shi zuwa shugaban majalisar, wanda hakan ba karamin abin alfahari bane ga al’ummar Masarautar baki ɗaya.

Bugu da ƙari kuma, ya ce “Muna alfahari da Sanata Ahmed Lawan bisa bajintar da yayi na takarar kujerar shugaban ƙasa, a jam’iyyar APC a zaɓen fidda-gwani da ya gabata, tare da bayyana bakin-cikin rashin nasarar da ya yi a zaɓen.”

Ya ce, Hon. Bashir Machina gogaggen ɗan siyasa ne wanda ya samu nasarar zaɓen fidda-gwani a kujerar Sanatan Zone C, wanda bisa hakan ne muke bayyana cikakken goyon bayan mu gare shi domin samun nasara a babban zaɓe mai zuwa na 2023.

“Har wala yau muna kira ga dukan ya’yan jam’iyyar APC, harda na PDP da ke arewacin Yobe su goyi bayan Hon. Machina don samun gagarumar nasara a zaɓe mai zuwa.

Kuma ina kara baku tabbacin cewa mu da matasa tare da dattawan mu a wannan yankin zamu haɗa hannu waje daya domin ganin Hon. Bashir Machina ya yi nasara.”

A nashi ɓangaren, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Jakusko, Hassan Kaku Lawan ya bayyana cewa, “Wannan taro ne na nuna goyon bayan al’ummar Bade da Jakusko ga ɗan takarar kujerar Sanatan Arewacin Yobe, Hon. Bashir Machina, wanda ya haɗa kowane ɓangaren jama’a, a matsayin yadda suma al’ummar Machina da sauran ƙananan hukumomin wannan yankin suka nuna wa namu Sanata a baya; Sanata Ahmed Lawan, a shekarun da suka gabata.”

“A hannu guda kuma, al’ummar wannan masarauta ta Bade suna bayyana cikakken goyon bayan su ga takarar Hon. Bashir Machina, bisa makamancin irin wannan goyon baya da suka samu daga masarautar Nguru da Machina a lokutan da Sanata Ahmed Lawan ya da yuka yana riƙe da kujerar majalisar dattawan yankin, saboda haka muna goyon bayan sa ɗari-bisa-ɗari.”

Shima tsohon muƙadashin sakataren tsohuwar jam’iyyar ANPP a jihar Yobe, Mohammed D. Sa’idu (Gaskanta) ya tofa nashi albarkacin baki da cewa, “Kamar yadda kace cin tuwon kishiya ramako, ko shakka babu haka zancen yake.

Saboda kimanin shekaru 16 da suka gabata, ita ma masarautar Nguru ta riƙe kujerar sanatan arewacin Yobe, wanda an shirya wannan taron ne domin bayyana goyon bayan al’ummar Bade da Jakusko ga takarar Hon. Bashir Machina a matsayin rama haɗin kai da goyon bayan da suka nuna mana a wadannan shekaru ga Sanata Ahmed Lawan.”

A nashi bayanin, shugaban taron kuma tsohon kwamishina a ma’aikatar wasanni da matasa ta jihar Yobe, Mallam Saleh Kachalla ya bayyana maƙasudin taron da cewa, “A matsayinmu na al’ummar Bade da Jakusko; makyasudin shirya wannan gangamin shi ne domin bayyana goyon bayan mu ga takarar kujerar sanatan arewacin Yobe wadda Hon. Bashir Sharif Machina zai yi, muna yi mashi fatan alheri tare da samun goyon bayan mu a babban zaɓe mai zuwa a 2023.”

A hannu guda kuma, kwamitin yakin neman zaɓen Hon. Bashir Sharif Machina ya karyata bayanan da ke yawo a kafafen sada-zumunta na zamani cewa Hon. Bashir Sharif Machina ya janye takararsa, wanda kwamitin ya bayyana wannan zance maras tushe da makama, tare da sake tabbatar wa jama’a cewa har yanzu ɗan takarar yana nan kan bakarsa na ɗan takarar sanatan arewacin Yobe a zaɓen 2023 mai zuwa.

A wata sanarwar manema labaru mai ɗauke da sa-hannun shugaban kwamitin, Alhaji Shehu Riga, ya bayyana cewa, “Babu wani lokaci a kowane yanayi da Hon. Machina ya taɓa sanya hannu ko bayani dangane da batun janyewa wani takarar da yake na kujerar sanatan arewacin Yobe. Saboda haka muna kira ga jama’a su yi watsi da wannan jita-jitar maras tushe da makama.”

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *