November 17, 2026

Cin Hanci Da Rashawa Na Kara Illata Najeriya A Mulkin Buhari – Melaye.

0

Dan majalisar wakilan Najeriya da ya je har sau biyu kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sanata Dino Melaye ya yi Allah-wadai da yakin yaki da cin hanci da rashawa na shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce maimakon gwamnati ta kashe cin hanci da rashawa, cin hanci da rashawa ne ke kara kashe ta (Najeriya).

Melaye a wata sanarwa da ya aikewa jaridar LEADERSHIP a ranar Lahadi, ya yi zargin cewa shugaba Buhari ya gaza wa ‘yan Najeriya da suka zabe shi a 2015.

A cewar sanarwar mai taken, ‘Tsawon lokacin da shugaban kasa ya dauka dole a yaki rashawa, kafin cin hanci da rashawa ya kashe Najeriya,’ Melaye ya bada rahotannin gida da waje da dama da kuma wasu kararraki da ya yi nuni da gazawar gwamnatin na yaki da cin hanci da rashawa.

“’Yan Najeriya ba za su taba mantawa da kalaman da Shugaban kasa ya yi a lokacin yakin neman zabensa a 2015 da yake cewa, ‘Dole ne mu yaki cin hanci da rashawa, kafin cin hanci da rashawa ya kashe Najeriya.’ Ya mai girma shugaban kasa, labaran da ake yadawa a yau shi ne, ‘Ba ka kashe rashawa ba; cin hanci da rashawa yana kashe Najeriya.’

“A ƙarshe, don haka, babu wata shaida dake nuna wani tabbataccen sakamako ko dai a yaƙi da rashin tsaro a ƙasar nan ko kuma a yaƙi da cin hanci da rashawa. Rashin tsaro na ci gaba da addabar al’ummomi da dama a Najeriya, makarantu na ci gaba da fuskantar rashin tsaro musamman a wasu sassan jihohin arewa maso gabas, ana kai hare-hare kan ofisoshin hukumar zabe da na ‘yan sanda a jihohin Gabashin kasar, yayin da sace-sacen mutane da garkuwa da mutane ya yi kamari a jihohin kudu maso yammacin kasar da sauran yankuna.

“Kimar Najeriya a cikin kididdigar cin hanci da rashawa da kungiyar Transparency International ta fitar na ci gaba da tabarbarewa. Ana ci gaba da wawure dukiyar kasa a karkashin gwamnatin shugaba Buhari.

“Wadanda suka zabi Buhari, suna tunanin cewa sun kafa sarkin yaki da cin hanci da rashawa, a yanzu suna cikin wadanda aka saba ma alkawali.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *