September 18, 2026

Yan Bindiga Sun Sace Mutane A Gwarinpa, Abuja.

0

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari da safiyar yau Litinin a gidajen rukunin zamani na Gwarinpa dake babban birnin tarayya Abuja.

Jaridar Dailytrust ta bada rohotan cewa, ‘yan bindigar sun kai farmaki a gidan ne tsakanin karfe 1 na dare zuwa karfe 4 na asuba, inda suka yi awon gaba da wasu mutanen da har yanzu ba a tantance adadinsu ba.

Ko da yake har yanzu babu cikakken bayani, wani mazaunin wurin Mohammed ya ce ‘yan bindigar sun shiga rukunin gidajen da ake cema “Estate Efab Queens” dake 6th Avenue, Gwarinpa.

Ya bayyana wa wakilin jaridar ta wayar tarho cewa, ’yan bindigar na dauke da baka, da kibiyoyi, da adduna kuma suna da yawa.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta shaida wa jaridar DailyTrust cewa, batun fashi da makami ne, ba na garkuwa da mutane ba.

Adeh ta ce tuni aka tura ‘yan sanda zuwa wurin domin gano yadda lamarin ya faru.

Ta ce, za a yima jama’a karin bayani kan lamarin daga baya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *