September 18, 2026

Ban Fito Takara Don Janyewa Ahmed Lawan Ba- In ji Hon. Machina

0

Daga M. Shamsudeen, Yobe

Ɗan takarar majalisar dattawa a mazaɓar Arewacin Yobe (Zone C), a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Hon. Bashir Machina, ya karyata jita-jitar da ke cewa ya sayi tikitin ɗin takarar ne domin janyewa shugaban Majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan, idan ya faɗi a zaɓen fidda-gwani.

Bashir Machina, wanda shi ne tsohon shugaban hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta Nijeriya (Nigerian Shippers Council), ya bayyana hakan a hirarsa da manema labaru inda ya ce wannan jita-jita ce maras asali da tushe kuma kirkirarre wanda kuma karya ce tsagwaronta.

Jita-jitar ta ci gaba da nuna cewa, har yanzu Sanata Lawan; ɗan takarar shugaban ƙasa, ya na hararar kujerar sanatan arewacin Yobe wadda Hon. Machina ya samu nasarar ta a zaɓen fidda-gwani, kana kuma aboki na kut-da-kut ga Gwamna Mala Buni.

Jita-jitar ta ci gaba da cewa, Hon. Machina, zai hakura ne ya barwa Sanata Lawan idan ya fadi a zaɓen fidda-gwani a takarar kujerar shugabancin ƙasa, a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Kamar yadda ya gabata, Bashir Machina shi ne ya samu nasara a zaɓen fidda-gwanin takarar kujerar babu hamayya, wanda tun kafin lokacin zaɓen wasu daga cikin masu abokanan hamayya suka janye masa, wanda wannan ya na ɗaya daga cikin abubuwan da suka hura wutar wannan jita-jitar domin janyewa Lawan cikin sauki kamar yadda yake a sashe na 35 a dokar zabe (Electoral Act).

Dangane da wannan batu, Hon. Machina ya fayyace cewa, “Na yi imanin cewa Dr. Ahmed Lawan ne kadai zai bayar da wannan amsar, amma domin kore shakka kan jita-jitar, kowa ya sani cewa shugaban majalisar dattawa bai sayi tikitin ɗin tsayawa takarar Sanata ba, face kawai na shugaban ƙasa ya saya.”

“Sannan kuma a tawa fahimta, shi kawai ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa ne, daga yankin Arewa, saboda haka wannan jita-jita karya ce kuma maras tushe da makama.”

Hon. Bashir Machina tsohon ɗan majalisar wakilai ne, a jamhuriya ta uku, wanda ya sha alwashin yin aiki tukuru domin ɗaukar matakan rage barazanar gurgusowar hamada a yankinsa tare da kirkiro hanyoyin da zasu taimaka domin alkinta saharar ta koma samun hanyoyin kuɗin shiga, wanda zai sa al’ummar yankin za su ci gajiyarta.

“Kamar yadda ka sani, jihar Yobe na ɗaya daga cikin jihohin da ke fuskantar matsalar hamada a Nijeriya. Sannan a matsayina na ɗan wannan yankin da ke fama da gurgusowar hamada, zan yi aiki tukuru wajen kawo kudurin dokar da zai kai ga sauya fasalin alkaba’in hamada zuwa hanyoyin samun kudin shiga ga jama’ar mu.

Musamman ta la’akari da kasashe irin su Israel, Canada, da Dubai sun riga sun yi nisa kan hakan, kuma muma zamu iya yin hakan.” Ta bakin Machina.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *