Malamai 9,204 ne suka rubuta jarabawar kwarewa ta majalissar malamai ta Najeriya.
Mukaddashiyar daraktan sashen bada takardar shidar kwarewa da lasisi Dr. Jacinta Ogboso ce ta bayyana hakan a Abuja a lokacin da take zagayawa, tare da duba yadda jarabawar ke gudana a makarantar SALSCON International School dake a Abuja.
Ta ce jumillar malamai 9,204 suka zauna jarabawar a fadin kasar nan, banda jihohin Zamfara da Sokoto saboda matsalar tsaron da suke fama da ita.
A wani labarin kuma, majalissar zata sake sanya ranar rubuta jarabawar a jihohin na Zamfara da Sokoto.
Dr. Ogboso ta bayyana cewa malamai 125 suka yi rijistar rubuta jarabawar a jihar Sokoto, yayinda malamai 51 ne suka yi a Zamfara.
Ta kara da cewa, za a gudanar jarabawowin a jihohin 2 idan yanayin tsaro ya inganta.
Tunda farko, saida babban sakatare a ma’aikatar ilimi ta FG David Adejo, wanda shima ya duba yadda jarabawar ke gudana a makarantar ta SALSCON International School, ya ce malaman da basu yi rijistar rubuta jarabawar ba basu cika malamai ba.
