September 17, 2026

Anbaliyar Ruwa: An Bukaci Yan Najeriya Su Shirya Ma Daminar Bana.

0

Hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya ta yi kira ga yan kasa da su daukar ma daminar bana matakan kaucema ambaliyar ruwa.

Shugaban hukumar Professor Mansur Bako Matazu ya yi wannan kiran a cikin wani sakon fatan alkairi da ya gabatar a wurin wani taron da aka shirya akan illar da ke tattare da ambaliyar ruwa na wannan shekarar da hukumar NEMA ta yi a Abuja.

Ya ce za a samu ruwan sama daidai-wadaida a wurare da dama na kasar nan cikin wannan shekarar, saidai za a iya samun ambaliyar ruwa.

Professor Matazu ya ce shekaru da dama Najeriya na shaida tsanantar yanayi, ruwan sama mai yawa, tsawa, da suke zuwa bayan iska mai karfi.

Kamar yadda hukumar kula da hasashen yanayin ta Najeriya ta bayyana, matsananci yanayin na yin illa ga rayuwar mutane saboda haka jan kunnen keda mahimmanci.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *