Karamar Hukumar Bindawa Ta Doke Mani A Gasar Mahawara.
Daga Auwal Isah
Sakataren ilimin karamar hukumar Mani ya shawarci yara yan makaranta a yankin da su maida ma karatunsu hankali yadda ya kamata.
Usman Umar Muduru ne ya bada wannan shawarar a lokacin gudanar da gasar mahawara tsakanin kananan hukumomi da aka fi sani da “debate” a turance.
Kamar yadda ya bayyana, gasar yan makarantar primaryn da aka shirya ma daliban makarantun Mashi, Ingawa, Dutsi, Bindawa da kuma karamar hukumar Mani nada nufin ganin an bunkasa kwazansu.
Sakataren ilimin ya ce gasar mahawarar nada nufin zabo daliban da suka fi kokari don su wakilci kowace karamar hukuma a matakin jiha.
A jawabansu na daban daban, jami’in shiyya na karamar hukumar Mani, Mashi, Bindawa Abdullahi Doka da kuma jami’in kula da gasar Ahmed Bala Mashi sun yi kira ga iyaye da su bada gudunmuwarsu cikin gasar ta hanyar bincikar kokarin yayansu idan sun dawo gida.
A karshen gasar mahawarar da ta gudana a karamar hukumar Ngawa, Allah ya ba karamar hukumar Ngawa sa’ar doke takwararta ta Dutsi.
Yayinda a wadda aka yi a karamar hukumar Mashi, Bindawa ce ta samu nasarar doke Mani.
Kuma yan makarantar primary ukku ukku ne suka wakilci ko wace karamar hukumar.
