September 18, 2026

Kungiyar Masu Sayar Da Babura Ta Koka Kan Rashin Matsugunni A Daura.

0

Daga Auwal Isah

Kungiyar masu sayar da babura reshen masarautar Daura ta koka kan rashin samun wurin dindindin da zasu ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu yadda ya kamata a yankin.

Sakataren kungiyar Salisu Amadu ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar wasu sabbin membobin kungiyar da aka tantance a Daura.

Ya yi nuni da cewa, kungiyar nada mahimmanci wurin bunkasa tattalin arzukin mutanen jihar nan.

Ya roki gwamnatin jihar Katsina da shugaban kananan hukumomin Daura da su samar ma kungiyar da wurin na dindindin.

Kamar yadda ya bayyana, kungiyar nada membobi sama da 100 a kananan hukumonin Mashi, Dutsi, Sandamu, Baure, Zango da kuma Mai’adua.

A tsokacinshi, shugaban kungiyar Abba Yusuf Daura ya hori sabbin membobin kungiyar da su bi dokoki da ka’idojinta.

Ya ce kungiyar ta tantance membobin yadda ya kamata kafin ta saka su cikin yayanta.

Da yake yin tsokaci akan lamarin, shugaban taron Imam Aminu Ahmed ya ja hankalin membobin da cewa su ji tsoran Allah.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *