Rev Fr. Joseph Bako, Ya Mutu Wurin Masu Garkuwa.
Wani Limamin Katolika, Rev Fr. Joseph Aketeh Bako, ya mutu a hannun wadanda suka yi garkuwa da shi makonni takwas bayan sace shi.
Shugaban Archdiocesen Katolika na Kaduna, Rev Fr. Christian Okewu Emanuel, ya bayyana hakan a ranar Laraba a Kaduna.
Idan ba a manta ba, an yi garkuwa da marigayi Rabaran Bako a gidansa da ke unguwar Kudenda a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a ranar 8 ga Maris, 2022.
Shugaban ya kuma bayyana cewa marigayi Fr. Bako ya mutu tsakanin ranar 18 ga Afrilu zuwa 20, 2022.
“An yi garkuwa da Joseph mai shekaru 48 a gidansa, a cocin St John Catholic Church Kudenda, inda yake hidima a matsayin limamin coci, a ranar 8 ga Maris, 2022, “in ji shi.
A cewar Fr. Bako ya yi rashin lafiya kafin a sace shi, kuma wadanda suka sace shi ba su bar shi ya tafi da magungunansa ba.
Jaridar LEADERSHIP ta ce, Ya kara da cewa, “An kashe dan uwansa a wurin sa, bayan an kashe dan uwansa kuma sai ya mutu.
“Ba mu samu gawarsa ba, amma mun tabbatar da mutuwarsa kuma mutanen da aka yi garkuwa da su tare suka sheda hakan.
Ya kuma kara da cewa limamin Katolika na Kaduna, Most Rev. Matthew Man-Oso Ndagoso, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalin Bako da dukan mutanen Katolika.
