September 18, 2026

Zargin Badaƙala: Sau Biyu Kawai EFCC Suka Taɓa Gayyata ta – Mustapha Inuwa

0

Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyar APC Dakta Mustapha Inuwa ya bayyana cewa tunda yake a rayuwarsa sau biyu kawai hukumar yaki da masu yi wa arzikin ƙasa ta’anati wato E’FCC ta gayyace shi akan wasu batutuwa.

Dakta Mustapha Inuwa yana wannan bayani ne a lokacin da ake tattaunawa da shi a gidan rediyon vision FM Katsina a cikin wani shiri mai suna ‘Babar Magana’ wanda kuma ya i dogon bayani game da wannan batu.

Ɗan takarar wanda ya ce masu tsoron shi ya fito takara ne suke yaɗa wannan magana saboda suna tsoron sa a wannan takara ta gwamnan jihar Katsina da ya fito.

Haka kuma ƙara da cewa tun lokacin gwamnatin marigayi Umaru Musa Yar’adua an taɓa gayyatarsa ofishin E’FCC tun suna Legas kuma ya je ya bada bayani har zuwa yau ɗin nan babu wanda ya ƙara tuntuɓarsa akan batun.

“Haka kuma kamar shekara biyu zuwa ukuvda suka wuce wani Abdulmumini Shehu Sani Store ya rubuta koke akan ofis ɗina zuwa ofishin E’FCC da ke Kano shima sun gayyace mu mun je mun ba su bayani har zuwa yanzu da nake wannan magana babu wanda ya ƙara waiwayata akan wannan batu” in ji shi.

Kazalika Mustapha Inuwa ya ƙara da cewa suna ICPC sun zo Katsina domin yin bincike kuma sun bincike an ba su bayani a rubuce inda suka ce duk jihohin Najeriya da suka bincika babu inda suka samu bayanai a cikin tsari kamar jihar Katsina.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *