Sanata Babba Kaita Ya Fice Daga APC Zuwa Jam’iyyar PDP
Rohotanni da ke zo mana na nuni da cewar, Sanatan Katsina ta Arewa wanda yake yankin da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya fito, Sanata Ahmad Babba Kaita ya fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP.
Rahotanni sun nuna cewa Babba Kaita ya miƙa takardar ficewa daga APC a mazaɓarsa ta Galadima ‘A’ da ke ƙaramar hukumar Kankia a Jihar Katsina.
Daga nan kuma an samu wani Video da aka hangi Sanata Ahmed Babba Kaita ya ziyarci jiga-jigan Jam’iyyar PDP na Jihar Katsina a gidan gona na Dattijon Jam’iyyar APC, Alhaji Hamisu Gambo Ɗan Lawan Katsina.
Hakan dai ya tabbatar da cewar Ficewar Sanatan daga APC ta tabbata zuwa PDP.
Masu Karatun Popular News Hausa menene Fatan Ku Ga Sanata Ahmed Babba Kaita?.
