Yafewa Dariye Da Nyame Haɗa Kai A Aikata Laifi Ne – DIG Osayande.
Mukaddashin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya (DIG) Parry Osayande mai ritaya, ya yi Allah-wadai da afuwar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa wasu gwamnonin jihar Filato, Joshua Dariye da Jolly Nyame na jihar Taraba, yana mai bayyana shi a matsayin hada kai a aikata laifi.
Da yake zantawa da manema labarai a birnin Benin na jihar Edo a wannan Alhamis din, tsohon mukaddashin babban aufeton ‘yan sandan Najeriyar ya kuma yi kira ga matasan Najeriya da su fito da yawansu domin kada kuri’ar da ta dace a zaben 2023 musamman ganin an kafa sabuwar dokar zabe.
Ya kuma bayyana goyon bayansa ga kiran da kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta yi na cewa shugaba Buhari ya yi murabus bayan ya gazawa wajen kare rayukan ‘yan Najeriya.
