September 17, 2026

Ramadan Iftar: Burina Shine Naga An Karfafawa Mata – Maryam Mai Rusau.

0

Daga Abdullahi Alhassan Kaduna.

Shugaban Mata a Jami’yyar APC ta Jihar Kaduna Hajiya Maryam Sulaiman wacce akafi sani da Mai Rusau,tace burin ta shine taga an Karfafawa Mata, Kasan cewar su Iyayen Al’umma bugu da kari kuma masu taka muhimmiyar rawa wurin kafa gwamnati a ko wani mataki a kasar nan.

Hajiya Maryam Mai Rusau,ta bayyana haka ne jim kaɗan bayan ta gama bude baki da Kungiyoyin Mata a Sakatariyar jam’iyar A P C dake Kaduna, inda ta

kara da cewar ta kira wan nan taron ne don ganawa da Mata Kasan cewar su,masu taka muhimmiyar rawa wajen ganin an cimma nasarar a kan kowani al’amari Aruwan nan bawai kawai zabe bama.

Mai Rusau, ta kara da cewar “mun wayar masu da kai kan mahimmanci karbar kati zabe kasan cewar zabe na kara karantawa, haka kuma mun karbi korafe- korafen su, kan yarda tafiyar aka yi ta a baya,inda muka yi alkawarin aiwatar da abinda zai kawo cigaba a wan nan karon.

Hajiya Maryam Mai Rusau, ta kuma bayyana irin Shirye Shiryen da Jam’iyar APC take dashi kan tallafawa Mata da Sana’o’i don su zama masu dogaro da kansu tare kuma da basu Jali don ganin sun habbaka Sana’o’in da suka koya.

Daga karshe tayi kira da yan Siyasa dama Masu hannun da shuni kan tallafawa Mata, musamman ma wadan da gaskesuka rasa mazajensu,ta hanyar daukar nauyin koyar dasu Sana’o’in daban -daban.

Ita kuwa a nata jawabin Shugaban Mata ta jam’iyyar APC shiya ta biyu Hajiya A’isha Idris yabawa kokarin Shugaban Matar tayi na ganin cewa an Karfafawa Matan kasan cewarsu jigo a tafiyar da jam’iyyar ,tare kuma da fatan cigaba da karfafawa matan kwarin gwiwa ta hanyar koyar dasu Sana’o’in da zasu dogara da kan su.

Su kuwa mahalarta taron bude bakin da shugabar Matan ta shirya yabawa shugabar Mata ta jam’iyyar APC din sukayi na ganin ta haɗa kansu tare kuma da jin korafe- korafen su don ganin an sauya salon gudanar da Jam’iyyar a jihar Kaduna.

Taron dai ya samu halartar Kungiyoyin Mata daga Shiyoyi uku da ake dashi na Siyasa a jihar Kaduna.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *