Zamu Gano Dalilin Ɗauke Jami’an Tsaro Daga Garin Shinfiɗa -Hon.Ɗanlami
Daga El-Zaharadeen Umar
Gwamnatin jihar Katsina ta kudiri aniyar gano dalili da kuma musababin ɗauke jami’an tsaro daga garin Shinfiɗa da ke cikin ƙaramar hukumar jibiya ta jihar Katsina.
Kwamishinan ma’aikatar harkokin jin daɗi da walwala da wassani na jihar Katsina Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da yake raba kayan abinci a garin unguwar Rinji ta gundumar Madarunfa a jamhuriyar Nijar.
Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya ce gwamnati ta damu so sai da halin da mutanen shinfiɗa suka shiga wanda hakan yasa ta dukufa wajan gano musababin ɗauke jami’an tsaron da ke wannan yanki domin bada kariya daga ‘yan ta’ada.
Kamar yadda Kwamishina ya bayyana wannan shine karo na huɗu da gwamnati ta ƙaddamar da rabon kayan abinci ga waɗanda wannan iftila’i ya faɗawa a lokutan baya.
“Gwamnatin Aminu Bello Masari ta bayar da tallafin kayayyakin abinci karo na hudu wanda yawanshi ya kai buhu dubu 100 ga al’ummar garin Shinfiɗa.” Inji shi
Haka kuma kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnati na ƙoƙarin ganin ta ziyarci wannan gari na Shinfiɗa domin tantance irin asarar da aka tabka a ya yin kai hare-haren ‘yan bindiga domin ɗaukar matakan gyara a gwamnatance.
Daga karshe Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya godewa hukumomin da ke gundumar Madarunfa na jamhuriyar Nijer akan yadda suke ta dawainiyya da wannan mutane da suke gudun hijira a garuruwan na su.
