An Yi Mini Rashin Adalci a APC Duk Da ƙoƙarin Da Na Yi – Rashida Mai Sa’a
Daga MUKHTAR YAKUBU.
Fitacciyar Jaruma a Masana’antar Kannywwod, Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a wadda baya ga kasancewar ta ‘yar fim za a iya cewa ita kadai ce Mace da ta shiga siyasa har ma ta tsaya takarar Shugabancin Mata reshen Arewa maso yamma a zaben da za a gudanar a Karshen wannan satin.
Sai dai tun kafin a shiga zaben Jaruma Rashida Adamu Abdullahi, ta bayyana irin rashin adalcin da aka yi Mata in da lokaci guda ba tare da an tuntube ta ba sai kawai ta ji an Kai wannan kujerar da take nema zuwa Jihar Sokoto alhalin ita Kuma ta fito daga Kano ne.
Ganin yadda abin ya fusata Jarumar ne ta yi taron ‘Yan Jarida domin bayyana irin rashin adalcin da aka yi Mata.
Rashida Adamu Abdullahi ta ce “Duk da irin gudummowar da muke bayarwa a tafiyar nan kuma wannan takarar ba ni na nema ba, mutane suka ga cancanta ta suka tsayar da ni Amma sai kawai muka ji an sauya abin ba tare da an sanar da ni ko jama’a ta ba, don haka mu ke ganin ba a yi mana adalci ba. “in ji Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a.
