Turka Turkar Gyaran Dokar Zaɓe: Babban Lauya Femi Falana Yace Kotu Ta Yanke Hukunci Bisa Kuskure
Dokar Zaɓe sashi na Tamanin da Hudu Sha biyu cikin baka 84 (12) tana kan dai dai kuma hukuncin da Kotu tayi yana akan Kuskure cewar Babban Lauya Femi Falana SAN
Wata Kotun Gwamnatin Tarayya ce dai dake da Zaman ta a Umuahia, Jihar Abia ta baiwa Ministan Shari’a na Najeriya damar ya cire wannan sashin daga cikin Sabuwar dokar da gaugawa.
Mai Shari’a Justice Evelyn Anyadike ce ta bayyana cewa sashin baya cikin kundin tsarin Mulkin Najeriya baida mazauni kuma baya bisa tsarin doka Dan haka an gogeshi ba zai samu wurin zama ba domin yayi cin karo da kundin tsarin Mulkin Najeriya.
Ita dai wannan Sabuwar dokar zaɓe tace babu wani mai riƙe da Muƙamin Siyasa a kowane Mataki ko a Gwamnatin Tarayya ko ta jihar da zai yi zaɓen Delegate ko kuma a zaɓe shi yayin taron Jam’iyya na kasa wato convention ko kuma congress na kowace Jam’iyyar Siyasa, da niyyar tsayawa Takarar kowace irin Kujerar Shugabanci, duk Mai Buƙatar hakan toh yazama wajibi ya ajiye Muƙamin da yake Kai da Watanni Shidda kafin zaɓe.
Karar Mai Lamba FHC/UM/CS/26/2022, Mai Shari’a Justice Anyadike ta ƙara da cewa sashi 66(1)(f), 107(1)(f), 137(1)(f) da 182(1)(f) na kundin tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya bayyana cewa Ma’aikacin Gwamnati da yake Buƙatar tsayawa Takara Toh zai ajiye Aikin shi ne ƙwanaki Talatin 30, kafin zaɓe, cewa duk wata doka saɓanin wannan wadda zata tursasa wani ya ajiye Muƙamin shi toh tayi cin karo da kundin tsarin Mulkin Najeriya.
Da yake ƙarin haske akan Lamarin Babban Lauya Mai zaman Kansa Femi Falana SAN yace wannan Hukuncin an yanke shine bisa Kuskure, domin shi kundin tsarin Mulkin Najeriya yayi Magana akan Ma’aikatan Gwamnati ko na Tarayya ko na Jiha ba waɗanda aka Naɗa ba.
Falana yace bisa sashi na 318 na kundin tsarin Mulkin Najeriya baiyi bayani akan Wani Mai Muƙamin Siyasa ba sai dai Ma’aikatan Gwamnati, Dan haka sashi na Tamanin da Hudu na Sabuwar dokar zaɓe yana nan kuma hukuncin da akayi anyi shine bisa Kuskure.
Ya ƙara da cewa , “ Idan akayi duba da waɗannan sassan na kundin tsarin Mulkin Najeriya lallai mai Shari’a tayi Babban Kuskure wajen yanke hukuncin 66 (1) (f), 107(1) (f),137 (1) (f) and 182 (1) (f) domin waɗannan sassan da mai Shari’a tayi amfani dasu suna Magana ne akan Ma’aikatan Gwamnati ba masu riƙe da Muƙamin Siyasa ba.
