Gidan Radiyo Najeriya Kaduna Ya Zama Wajan Adana Tarihi Da Al’adun Arewa – Sarkin Kano
Daga Babangida Sunusi, Kano
An bayyana gidan Radiyo tarayyanTarayya na Kaduna a matsayin wurin da ya dade yana adana al’adun arewa da tarihi na tsawon lokaci a ƙasar nan.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mai martaba Sarkin Kano Alh, Aminu Ado Bayaro, a wata zantawa da wakilin gidan Radiyo a jiya laraba kan batun cikar gidan rediyon shekaru 60 da kafuwa.
Mai martaba Sarkin Kano ya kuma ƙara da cewa lallai za’a kwashe shekaru ana amfana da ayyukan wannan tasha mai tarin albarka da amfanar da jama’a.
Sarkin ya cigaba da bayyana tashar rediyon tarayya na Kaduna babu shakka ya kasance wani jigo na hada kan al’ummar ƙasar musamman lokutan da a kayi yakin basasa da wasu rikice-rikice da suka faru.
Sannan ya jadadda cewa wannan kafa yada labaran ya dade yana fadakar da jama’a hadi da ilimantarwa akasar na tsawon shekaru sittin dasuka fara gabatarda shirya-shiryensu.
Aminu Ado ya kuma bukaci gwamnati da ta shigo ciki wajen samar ma da wannan kafa kayan aiki na zamani da inganta walwalar ma’aikatan dake aiki agidan dan daukaka matsayin kasar nan.
Sarkin yace lallai tun tasowarsu basu san wani gidan Radiyo kamarsa ba wajen faɗakar da al’umma, dan Kuma su kansu sun samu riba wajen sauraren wannan gidan radio da bada bada sahihan labarai da duk wanda yake kasar nan bama arewaba kadai.
Sannan ya ƙara tabbatar da cewa wannan gidan Radiyo yaf i dukkannin wasu kafofin sadarwa na zamani muddun a kasamo hanyar da za’a inganta rayuwar matasa da tsamosu daga matsalar da ke faruwa a halin yanzu da da yawan matasa suna fadawa ciki.
Daga karshe mai martabar ya bayyana taya ma’aikatan gidan Radiyo murna bisa yadda suke gabatar da shirya-shiryensu a tsawon shekaru 60 da fara aikin su.
