September 18, 2026

Zaɓan Ƙananan Hukumomi: Jama’a Ku Runguni Lafiya Da Lumana -Hukumar Shari’a Ta Jihar Katsina.

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Hukumar Shari’a ta jihar Katsina ta yi kira ga al’umma da su kasance masu bin doka da oda tare da rungumar zaman lafiya a lokacin gudanar da zaben ƙananan hukumomi da za a yi nan ba da jimawa ba.

Wannan kiran ya fito ne daga bakin shugaban hukumar Shari’a na jihar Katsina Khadi Muhammad Kabir a lokacin taron manema labarai da aka gudanar a Katsina.

Khadi Muhammad Kabir ya ce kiran ya zama wajibi idan aka yi la’akari da dokar tabbatar da zaman lafiya da gwamna Masari ya sanyawa a hannu a kwanakin baya. (Containment order)

Ya kuma Kara cewa wannan zaɓe na kananan hukumomi da ke tafe ya zama wajibi hukumar Shari’a ta jawo hankalin jama’a kan wasu mahimman al’amurra kamar haka;

Na ɗaya a fahimtar musulunci, zaɓuɓuka da hanyoyin gudanar da zaɓe, hanyoyi ne na ba ‘yan Ƙasa damar zaɓen waɗanda suke don su wakilce su wajan gudanar da shugabanci bisa shiryarwa Alkur’ani mai girma.

“A musulunci jam’iyyun siyasa da ‘yan siyasa da masu jefa kuri’a dukkannin su wajibi ne su kiyaye ƙa’idojin da dokoki da sharruɗan gudanar da zaɓe, game da tanade-tanade da ke cikin dokar tsaro da gwamna ya sanyawa hannu.” inji shi.

Ya ƙara da cewa abu na uku shi ne shari’ar Muslunci bata yarda da gudanar da duk wasu ayyuka na barna ko tada hankalin jama’a ko ɓata duniyoyi da sauran ayyukan ta’addanci ya yin gudanar da kowace irin hulɗa ko muaamula.

Haka kuma baban Khadi Muhammad Kabir ya kara da cewa a shari’a, waɗanda suke ayyukan barna da ta’addanci da sauran ayyukan banga ta siyasa ko makamanciyar haka domin muzgunawa jama’a ko tsoratar da su ko tada masu hankali ana ɗaukar masu irin waɗannan ayyukan barna a matsayin makiya Allah ta’ala.

Shugaban hukumar shari’a ta jihar Katsina ya cigaba da kawo ayoyin Alkur’ani da Hadisan Manzon Allah (S) game da bin doka da oda domin a zauna lafiya.

Daga karshe ya yi fatan cewa jama’a za su rungumi zaman lafiya da lumana a lokacin gudanar da zaben ƙananan hukumomi da kuma bayan an gama domin hakan shi ne zai kawo cigaba a cikin al’umma baki ɗaya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *