Badaƙalar Tsige Mataimakin Gwamna: Da Gaske Mahdi Aliyu Gusau Ya Bada Kudi Don Kar A Tsige Shi – Kanoma
Dan majalisar da ke wakiltar Maru ta Arewa a majalisar dokokin jihar Zamfara Yusuf Alhassan Kanoma ya tabbatar da cewa wasu abokan aikinsa sun karbi kudade dalar Amurka kan tsige mataimakin gwamna Barr. Mahadi Aliyu Gusau.
Kanoma wanda ya bayyana cewa makasudin bada kudaden shine, don a dakile tsige tsohon mataimakin gwamnan, sannan yace ‘dan majalisar PDP da ya raba dalolin ya sani sarai cewa ba zai iya tunkararsa da cin hanci ba shiyasa bai ma fara ba.
Ya tabbatar da cewa wasu ‘yan majalisar da suka karbi kudaden daga baya sun kai wa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Zamfara kudaden, suka karbi takardar shedar sun gabatar da wadannan kudade ga hukumar, yayin da wasu kuma suka tafi da kudaden ba tare da bayyana su ba.
Ya ce duk da cewa an bayar da kudaden ne don cin hanci, amma ba za a hukunta mambobin ba saboda bayan an basu, sun gabatar da kudaden, kuma an basu ne bisa ga ra’ayin tsohon mataimakin gwamnan na dakile tsige shi.
Idan aka ba ni kudaden zan karba kuma in tabbatar da cewa an tsige Mataimakin Gwamna kuma, ban damu ba saboda wannan ita ce hanyar koya masa darasi.
Kanoma ya kara da cewa, abin farin cikinmu shi ne an fatattaki aniyarsa ta bayar da kudade, saboda ana so a kawo cikas ga shirin tsigewar, amma daga karshe anyi nasarar tsige Mahadi Aliyu Gusau.
