Za mu gama da Lakurawa nan ba da jimawa ba – Ribadu
Za mu gama da Lakurawa nan ba da jimawa ba – Ribadu
Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta tabbatar da kawo ƙarshen kungiyar yan ta’adda da ake kira ‘Lukarawa’ a shiyyar Arewa maso yammacin nan ba da jimawa ba.
Ribadu ya bayyana haka ne a lokacin da ya wakilci shugaban kasa Tinubu a wajen bikin bude babban taron kwastam na shekarar 2024, ranar Laraba, a Abuja.
“Za mu fatattaki wadanda ake kira Lukarawa daga kasarmu. Za mu kunyata masu sukar mu kuma zamu rufe bakunansu. Boko Haram da suka addabi kasarmu a baya, yanzu tserewa suke. Yanzu haka mambobinta suna tafiya zuwa wasu kasashe makwabta saboda basu da damar yin ta’addancin su a Najeriya” inji shi.
Ya kuma bayyana cewa, alamun na ƙara nuna cewa al’amura na cigana da inganta ta fuskar tattalin arziki a ƙasar nan wanda kowa zai iya gani, inda ya ba da misali da yadda ake hako danyen mai a yankin Neja-Delta da kuma sauye-sauyen kasafin kudi da babban bankin Najeriya (CBN) ke yi a cikin irin wannan kokari.
“Hakar danyen mai ya kai ganga miliyan 1.8 a kowacce rana. sannan kuma an tsaftace babban bankin kasa; babu wanda ke ɗaukar kobo daga babban bankin. Mun yi alkawarin cewa za mu gyara kasar nan, kuma za mu yi hakan domin Shugaba Tinubu bai taba zama mutum mai gazawa ba,” inji shi.
