2027: Ku Fara Tattara Kayanku Daga Gidan Gwamnati: Sakon PDP Ga APC Ta Katsina
2027: Ku Fara Tattara Kayanku Daga Gidan Gwamnati: Kashedin PDP Ga APC Ta Katsina
Sabon shugaban jam’iyyar PDP Hon. Nura Amadi Kurfi ya gargadi jam’iyyar APC mai mulki a jihar Katsina da ta fara tattara komatsanta daga gidan gwamanti kafin ranar zaɓen 2027
Hon. Nura Amadi Kurfi ya yi wannan hannunka mai sanda ne jim kaɗan bayan amsar rantsuwar kama aiki a matsayin sabon zaɓaɓɓen shugaban jam’iyyar PDP ɓangaren Sanata Yakubu Lado ƊanMarke
An fara rantsar da shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina Muhammad Nura Amadi Kurfi tare da sauran waɗanda za su shugabanci jam’iyyar tsawon shekaru huɗu masu zuwa
Duk a cikin jawabinsa Hon. Nura Amadi Kurfi ya yabawa shugabancin jam’iyyar PDP a matakin ƙasa ƙarkashin jagorancin Alhaji Umar Iliyasu Damagum wanda yake tafiyar da PDP a cikin wannan mawuyacin hali.
Alhaji Nura Amadi Kurfi ya kuma nuna godiyar sa ga jagoran tafiyar su, Sanata Yakubu Lado ƊanMarke wanda ya bayyana a matsayin wanda ya jagoranci nasarar da Atiku Abubakar ya samu a zaɓen 2023 a jihar Katsina
A cewar sa, jajircewa irin ta Sanata Yakubu Lado ita ce maƙasudin samun nasarar cinye zaɓen shugaban ƙasa da wasu ‘yan majalisun tarayya a lokacin zaɓen 2023 a jihar Katsina
Ya kuma ƙara da cewa Sanata Yakubu Lado shi ne mutum ɗaya da ya kasance madugun Yan adawa wanda yasa jam’iyyar PDP a jihar Katsina ta zama kwanli kura mai shiga idon masu mulki tare da tabbatar da jin dadi da walwalar mambobinta.
Sabon shugaban jam’iyyar PDP ya ce shugabancin su zai maida hankali akan abubuwa guda hudu da suka haɗa da tabbatar da haɗin kan ‘ya ‘yan jam’iyya da bin doka da oda da kyautata alaƙa da tafiya tare da kowa da kuma baiwa mambobi damar su taka rawa a fagen siyasa musamman a zaɓen 2027.
Kazalika Hon. Nura Amadi Kurfi ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a jihar Katsina da su bada goyon bayan da ake buƙata domin samun nasarar shugabanci da kai jam’iyyar mataki na gaba.
Tunda farko, a jawabin sa shugaban rikon kwarya na jam’iyyar PDP a jihar Katsina Malam Abdulkarim Musa Makarfi wanda ya jagoranci shirya zaɓoɓuka ya miƙa ragamar shugabanci a hannun sabbin shugabanni.
Haka kuma ya jagoranci rakiyar sabbin shugabannin Jam’iyyar PDP na jihar Katsina tare da dubun dubatar magoya bayan su zuwa ofisoshin su domin kama aiki gadan-gadan.
