September 18, 2026

2023: Babu Dalilin Da Zai Sa In ƙyamaci Bola Ahmad Tinubu Sarkin Sakin Katsina

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya bayyana cewa shi kam bai ga wani dalili da zai sa ace ya guji Bola Ahmad Tinubu game da kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Sarkin na Katsina yana wannan magana ne a lokacin da kungiya Arewa Orgasanition For Asiwaju’ (AROMA) suka kai masa ziyarar tuntuɓa dangane da batun takarar Bola Tinubu a fadarsa da ke Katsina.

Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya ce Bola Tunibu ya yi masa abin alheri a shekarun baya, musamman lokacin da za a yi wani taro a lokacin marigayi mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Kabir Usman, ya ce Tinubu shi kadai ne gwamnan da ya halarci wannan biki da aka shirya a Katsina.

“A wannan kokacin ina magajin garin Katsina, duk wani gwamna da ke Najeriya Bola Tinubu ne kadai ya zo wannan biki na mai martba Sarki, kuma mun samu labarin cewa daga sama aka bada umarnin hana gwamnoni zuwa Katsina amma shi Tinubu sai da ya zo, wannan yasa babu dalilin da zai hanani shiga cikin al’amuran sa.’ inji shi

Mai martaba Sarki ya kara da cewa tunda ya zama sarkin Katsina bai taba amsar baki a ranar jumaa ba, amma saboda mahimmcin tawagar Bola Tinubu yasa ya tsaya ga lokacin masallaci domin ya tarbi wannan tagawa kuma ya ji abinda ya kawo su.

Shima da yake bayyana dalilin zuwansu fadar mai martaba Sarkin Katsina, shugaban tawagar, Sanata Abu Ibrahim ya bayyanawa Sarkin cewa daga cikin manyan dalilan da suka sa suke san yan arewa su marawa Bola Tinubu baya domin kawo cigaba da maganin matsalar tsaro a wannan yanki na arewa.

“Fiye da shekaru talatin ina tare da Bola Tinubu nasan shi so sai, nasan abinda zai iya yi da wanda ba zai iya ba, mutun ne shi mai san arewa, saboda haka akwai alfano idan har aka zabe shi ya zama shugaban kasa a 2023” inji Sanata Abu Ibrahim

Ya kara da cewa kungiyoyi ne 37 suka hadu daga yankin arewa domin yin wannan tafiya ta Bola Tinubu kuma sun zo masarautar Katsina domin neman albarka da shawara daga manya irin su mai martaba sarkin Katsina.

Daga cikin yan tawagar akwai kakakin majalisar dokokin jihar Kano da yan siyasa da wakilan kungiyoyin da makusantan Bola Tinubu da suka zo domin fara sharar fage kafin shi uban gayyar ya isao da kansa.

Haka kuma sun kai ziyarar ban girma ga mahaifiyar tsohon shugaban Kasa Umaru Musa Yar’adua da kuma gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari a gidan gwamnati.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *