September 17, 2026

‘Ƴan Bindiga Sun Sake Tare Hanyar Abuja Zuwa Kaduna Da Tsakar Ranar Yau Alhamis

0

‘Yan bindiga masu tarin yawa sun sake tare hanyar Abuja zuwa Kaduna da tsakar ranar yau Alhamis.

Wannan na zuwa ne kwana huɗu bayan wani mummunan hari da ‘yan bindigar suka kai a kan jirgin kasa mai jigila tsakanin Kaduna da Abuja.

Sanata Shehu Sani ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, inda ya ce an kira an tabbatar mishi ‘yan bindiga masu yawan gaske sun sake tare hanyar.

“Na amsa wani kiran gaggawa, inda wasu matafiya suka sanar da ni cewar gungun ‘yan bindiga sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja da tsakar ranar yau Alhamis, wanda haka ya sa matafiya suka dinga juya wa da motocinsu a guje.” fasarar kalam Shehu Sani da ya yi a harshen Ingilishi.

Zuwa yanzu ba mu kai ga samun cikakken rahoton faruwar lamarin ba, amma za mu sanar da masu karatun yadda al’amarin ya faru da zarar mun samu cikakken rahoton.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *