Ɗaliban Musawa Da Matazu 1,991 Za Su Amfana Da Tallafin Karatun Naira Miliyan 32,500 A Katsina.
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Ɗaliban ‘yan asalin ƙananan hukumomin Musawa da Matazu masu karatu a manyan makarantun gaba da sakandare zasu amfane da tallafi daga gidauniyar ɗan majalisar tarayya Hon. Abdullahi Aliyu (Talban Musawa)
Wannan tallafi dai kimanin ɗalibai 1,991 da suka fito da mazaɓu 21 da ake da su a ƙananan hukumomin Musawa da Matazu kuma waɗanda suke Karatu a manyan makarantun gaba da sakandare.
Shugaban kwamitin ilimi na ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Ƙananan hukumomin Musawa dakta Samaila Adamu Dangani ya bayyana cewa wannan wani tallafi ne na gidauniya ɗan majalisar domin tallafawa iyaye da kuma ɗalibai.
Ya ƙara da cewa kimanin ɗalibai 1,087 ne suka fito daga ƙaramar hukumar Musawa a ya yin da 808 suka fito daga ƙaramar hukumar Matazu kuma dukkan su an tantance su, kuma sun tsallake ƙa’idojin da aka shinfiɗa
A cewar sa masu karatun digiri da babar difloma (HND) zasu samu tallafin naira dubu ashirin (20,000) sai kuma masu karatun NCE da ƙaramar difloma (ND) kowanensu zai samu dubu sha biyar (15,000)
“Inason in yi amfani da wannan damar in sanar da al’umma cewa tun farko, mun samu adadin ɗalibai 2,364 amma da aka yi aikin tantancewa shi ne mutane 1,991 suka samu nasara kuma sune za su amfana da wannan tallafi” inji Ɗangani
Dakta Samaila Adamu Dangani ya yi ƙarin haske da cewa wannan tallafi bai nuna bambanci siyasa ba, in dai mutum ya cancanta ko daga wace jam’iyya yake zai amfani in dai ɗan asalin ƙananan hukumomin Musawa da Matazu ne.
Tunda farko da yake jawabi gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya nuna jin daɗinsa da wannan tallafi da ɗan majalisa mai wakiltar Ƙananan hukumomin Musawa da Matazu Hon. Abdullahi Aliyu (Talban Musawa) ya bada.
Gwamnan wanda ya ce Hon. Abdullahi Aliyu na ɗaya daga cikin ‘yan majalisu da ya nuna sha’awar sa na tallafawa ɗaliban da suka fito daga ƙananan hukumomin Musawa da Matazu
” Ilimi na ɗaya daga cikin abubuwan da Abdullahi Aliyu ya baiwa fifiko saboda haka ne ma ya fara da ware wadannan makudan kudade domin ba ɗalibai tallafi, kuma hakan ya kamata ya zama tsani ga sauran ‘yan majalisun da ake da su a nan jihar Katsina” inji Dikko Raɗɗa
