Zauna A Gida: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Ga Shugaban Karamar Hukuma A Ebonyi, Sun Kashe Mutun hudu.
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a gidan shugaban karamar hukumar Ikwo na jihar Ebonyi Mr. Steve Orogwu a Ikwo.
Jaridar SUNNEWS ta ce, maharan sun mamaye gidansa ne a daren jiya Talata, amma baya gida.
A fusace saboda rashin ganinshi ‘yan bindigar suka bude wuta kan mutanen wurin, inda suka kashe ‘yan uwansa uku .
Majiyoyi da suka tabbatar da faruwar lamarin, sun shaida wa wakilin jaridar SUNNEWS cewa ‘yan bindigar sun kashe mutane hudun a yayin harin.
“Uku daga cikin wadanda abin ya shafa ‘yan uwan shugaban karamar hukumar ne, yayin da dayan kuma makwabcinsu ne. “Muna zargin sun zo ne domin neman shugaban, amma ba ya nan a lokacin,” daya daga cikin majiyar da ta nemi a sakaya sunanta ta ce.
Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi, Loveth Odah, ba ta ce komai ba kan lamarin har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.
