November 18, 2026

Zamu Riƙa Shirya Gasar Karatun Alkur’ani Duk Shekara Karkashin Gidauniyar Lamido -Hon. Jabiru Tsar

0

Zamu Riƙa Shirya Gasar Karatun Alkur’ani Duk Shekara Karkashin Gidauniyar Lamido -Hon. Jabiru Tsari

Shugaban ma’aikatan faɗar gwamantin jihar Katsina Malam Jabiru Abdullahi tsauri ya yi alƙawarin shirya gasar karatun Kur’ani duk shekara a jihar Katsina.

Shirya gasar na da nufin karfafa yara matasa masu kokarin haddace Alkur’ani mai girma tare da ware kyaututtuka ga waɗanda suka yi zarra a wajen gasar.

Jabiru Tsari Lamidon Katsina na farko ya bayyana haka ne a lokacin rufe wata gasar karatun Alkur’ani da aka shirya a ɗaya daga cikin bukukuwan shagalin naɗin sa matsayin Lamidon Katsina da Mai martaba Sarkin Katsina zai yi.

Gasar wanda wasu ɗalibai yan islamiyya suka shirya a matsayin gudunmawar su tare bada nuna murnar akan wannan naɗi na Lamidon Katsina ta samu shigatda dalibai da dama.

Hon. Jabiru Abdullahi tsauri ya ƙara da cewa duk acikin shirye-shiryen naɗin gidauniyar Lamido ta rarraba kayayyakin karatu ga dalibai ‘yan firamare a garin tsauri ta ƙaramar hukumar Kurfi.

“Sannan wannan gidauniya ta duba marasa lafiya domin ba su magunguna ƙarkashin kulawar kwararrun malaman kiwon lafiya duk a cikin garin tsarin” inji

Shima da yake nasa jawabin babban limamin masallacin Banu Kumasi Imam Samu Ali Bakori ya yaba da irin da ƙoƙarin da wannan gidauniya ta Lamido na tallafawa al’umma

Ya ƙara da cewa abu ne mai kyau a riƙa taimakawa waɗanda ba su da shi, musamman idan mutum ya samu dama a gwamnati haka ya kamata a riƙa.

Sai dai Imam Samu Ali Bakori yana mai ƙara jan hankali ga mahukunta musamman akan irin halin da masallatai ki ciki, inda ya yi kira da juya akan gyara da kuma inganta masallatan juma’a da kuma na sallolin yau da kullum.

Daga ƙarshe ya Jinjinawa Gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa akan alawus alawus da gwamnatin sa take baiwa limamai da ladanai a fadin jihar Katsina.

A shirya wannan kwarya-kwarya gasar karatun Alkur’ani ne a Mallacin Banu Kumasi da ke G.R.A cikin birnin Katsina.

Daga cikin waɗanda suka halarci wannan taro sun haɗa da mai Garin tsauri da Ɗan Burun ɗin Daura, Alhaji Daha Umar Faruƙ, Hon. Saboda Musa Hassan, Baban kwamandan Hisba na jihar Katsina Malam Abu Ammar da Hon. Abdullahi Darma da sauransu

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *