September 17, 2026

Zamu Ɗauki Matakin Shari’a Akan Masu Tsokanar Alhaji Rufa’i. Cewar Barista Abba Hikima

0

Jiya bayan wasu bayin Allah sun kai shi asibiti, likitoci sun tabbatar cewa tsokanar da ake yiwa Lawan Rufai (Alhaji Rufa’i) tana kara tunzura shi. Kuma hakan na kara masa rashin lafiyar dake damun sa.

Saboda haka duk wanda ya kara tsokana ko tunzura wannan bawan Allah, sai mun dauki matakin shariah a kan sa ko waye InshaAllah.

Wannan rashin tsari ne da sanin ya kamata. Inda dan’uwan masu yin hakan ne babu wanda zai bari a dinga wulakanta shi haka. Sai kace ba musulmi ba?

Allah ya bashi lafiya. Ameen.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *