Zaɓen 2023: Zamu Kawar Da Rashin Tsaro Da Cin Hanci Da Rashawa –Dr. Bugaje
Wani mai fafutukar siyasa kuma dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyar PRP Dr. Usman Muhammad Bugaje ya ce idan ya zama shugaban kasar Najeriya zai yi aiki tare da al’ummar Najeriya musamman wajen kawar da rashin tsaro, satar dukiyar kasa, da kuma yaki da cin hanci da rashawa a fadin kasar.
Dr. Usman Bugaje ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Mayu, 2023, a wata ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PRP ta jihar Katsina, inda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a babban zaɓe mai zuwa na gari 2023.
Dakta Bugaje ya kara da cewa, “Najeriya ba ta aiki, amma mafi muni har yanzu ita ce wuri mafi hadari a duniya, ya kuma bayyana ikonta na mulki ta hanyar sace-sace, almubazzaranci, mulkin kama karya da kuma cin hanci da rashawa.”
‘Al’adunmu na siyasa sun yi ta tafiya, sun bayyana da kuɗi maimakon mayar da hankali wajen farfaɗo da fannin kamar su tsaro, noma, tattalin arziki, ilimi, lafiya da dai sauran matsalolin da talakawa ke fuskanta musamman rashin aikin dogaro da kai,” inji shi. yace.
Ya ƙara da cewa waɗanda da suke riƙe da madafun iko ba a shirya suke ba wajan gyara wannan ƙasar saboda yadda suke yi al’umma rikon sakainar kashi.
Dakta Usman Bugaje wanda ya ce babu wani ɓangare a wannan ƙasar da ke tafiya daidai wanda ya ce dole jama’a su tashi tsaye wajan kawo canji mai ma’ana da zai amfani kowa.
